1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lallai Allah ba Ya karɓar aiki sai wanda ya zama abin tsarkakewa, kuma aka nufi fuskar Allah da shi

عَنْ أَبِي أُمَامَةَ الْبَاهِلِيِّ رضي الله عنه قَالَ:
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: أَرَأَيْتَ رَجُلًا غَزَا يَلْتَمِسُ الْأَجْرَ وَالذِّكْرَ، مَا لَهُ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا شَيْءَ لَهُ» فَأَعَادَهَا ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، يَقُولُ لَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا شَيْءَ لَهُ» ثُمَّ قَالَ: «إِنَّ اللَّهَ لَا يَقْبَلُ مِنَ الْعَمَلِ إِلَّا مَا كَانَ لَهُ خَالِصًا، وَابْتُغِيَ بِهِ وَجْهُهُ»

Daga Abu Umama al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Shin kana ganin mutum ya yi yaƙi yana neman lada da yabo, me gare shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba shi da komai". Sai ya maimaita masa sau uku, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ce masa: "Ba shi da komai" sannan ya ce: "Lallai Allah ba Ya karɓar aiki sai wanda ya zama abin tsarkakewa, kuma aka nufi fuskar Allah da shi".

Ingantacce ne Nasa'i ne Ya Rawaito shi Sunanu Nasa'i - 3140

Bayani

Wani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: dan ya tambaye shi ya nemi fatawarsa game da hukuncin mutumin da yake fita yaƙi yana neman lada daga Allah da kuma kwaɗayin yabo da godiyar mutane, shin zai samu lada? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bashi amsa: Da cewa bashi da komai na lada; dan abinda ya yi wa Allah tarayya da shi a cikin niyyarsa, sai mutumin ya maimaita tambayarsa sau uku ga Annabi - tsira da amincin Allaah su tabbata agare shi -, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana amsa masa wannan amsar; da cewa bashi da lada, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bashi labarin cewa ka'idar karbar aiki a wurin Allah: Lallai cewa Allah ba Ya karbar aiki sai in ya zama dukkansa saboda Allah ne batare da tarayya da wani a cikinsa ba, kuma ya zama dan zatin Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa -.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Allah ba Ya karɓar ayyuka sai abinda ya zama tsarkakakke ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da kuma dacewar shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agagtre shi -.
  2. Yana daga kyanwun amsa fatawar mai bada fatawa fatawarsa ta zama ta cika manufar mai tambaya da ma ƙari.
  3. Karfafa al'amari mai girma ta hanyar maimaita tambaya game da shi.
  4. Mai yaƙi na gaskiya shi ne wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, da kuma neman lada da sakamako na lahira tare da tsarkake niyya, badan yaƙinsa ya zama dan duniya ba.

Manufofin Fassarorin

51 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية