1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«خَيْرُ صُفُوفِ الرِّجَالِ أَوَّلُهَا، وَشَرُّهَا آخِرُهَا، وَخَيْرُ صُفُوفِ النِّسَاءِ آخِرُهَا، وَشَرُّهَا أَوَّلُهَا».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 440

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi alherin sahun maza a cikin sallah kuma mafi yawansu a lada da falala shi ne na farkonsu; dan kusancinsu ga liman da jinsu ga karatunsa da nisantarsu daga mata. Mafi sharrinsu kuma mafi ƙarancinsu a lada da falala, kuma mafi nisancinsu daga abin nema a shari'a shi ne ƙarshensu. Mafi alherin sahun mata na ƙarshensu; domin cewa yafi sutura garesu, kuma mafi nisanta daga cakuɗuwa da maza da ganinsu da fitinuwa da su, mafi sharrinsu na farkonsu; dan kusancinsu ga maza da bijirowa ga fitina.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitar da maza akan gaggawa zuwa biyayya da sahun farko a cikin salloli.
  2. Halaccin sallar mata a cikin masallaci tare da maza a cikin sahu mai zaman kansa, sai dai tare da suturtuwa da kamewa.
  3. Mata idan sun taru a cikin masallaci, to cewa su zasu zama sahu kamar sahun maza, kuma kada su rarrabu, kai wajibi ne su daidaitu a cikin sahu da toshe kafa, kamar yadda yake a cikin sahun maza.
  4. Bayanin tsananin kulawar shari'a ta hanyar kwaɗaitarwa da nisantar mata ga maza har a guraren ibada.
  5. Fifikon mutane a gwargwadan ayyukansu.
  6. AlNawawi ya ce: Amma sahun maza shi akan gamewarsa ne, to mafi alherinsa na farkonsa har abada, kuma mafi sharrinsu na ƙarshensu har abada. Amma sahun mata abin nufi da Hadisin: Sahun mata waɗanda zasu yi sallah tare da maza, amma idan zasu yi sallah daban ba tare da maza ba to su kamar maza ne; mafi alherin sahunsu na farkonsu kuma mafi sharrinsu na ƙarshensu.
  7. AlNawawi ya ce: Sahu na farko abin yabo wanda Hadisai suka zo da falalarsa da kwaɗaitarwa akansa shi ne sahun farko wanda yake bin liman; daidai ne ma'abocinsa ya zo ne da wuri ko a makare, kuma daidai ne, taƙaitawa ta ratsa shi ne da makamancinsa ko a'a.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية