1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ:
«اللهُمَّ لَكَ أَسْلَمْتُ، وَبِكَ آمَنْتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خَاصَمْتُ، اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِعِزَّتِكَ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْ تُضِلَّنِي، أَنْتَ الْحَيُّ الَّذِي لَا يَمُوتُ، وَالْجِنُّ وَالْإِنْسُ يَمُوتُونَ».

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa:
"Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, wannan lafazin na Muslim ne, amma Bukhari ya rawaito shi a taƙaice Sahih Muslim - 2717

Bayani

Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: (Ya Allah gareKa ne na miƙa wuya) kuma na jawu, (da Kai ne na yi imani) na gasgata kuma na yi iƙrari, (kuma gareKa ne na dogara) na fawwala na kuma dogara, (gareKa ne na koma) na koma na fuskanta, (saboda Kai ne na yi husuma) na yi jayayya da maƙiyanKa, (Ya Allah ni ina neman tsarinKa) ina fakewa (da buwayarKa) da hanawarKa da kuma rinjayenKa, (babu abin bautawa da gaskiya sai Kai) kuma babu wani abin bautawa da gaskiya inba Kai ba, (da Ka ɓatar da ni) daga shiriya da dacewa da yardarKa, (Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba) kuma ba zai ƙareba, (aljanu da mutane kuwa zasu mutu).

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin gabatar da yabo (ga Allah) a yayin roƙon kowane abin nema.
  2. Wajabcin dogara ga Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai da neman kiyayewa daga gareShi; domin cewa Shi Mai siffantuwa ne da siffofin cika, kuma Shi kaɗaine wanda ake dogara da Shi, halittu dukkaninsu gajiyayyu ne kuma masu tiƙewa ne zuwa ga mutuwa, su basu cancanci dogara a kansu ba.
  3. Koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin addu'a da waɗannan kalmomi masu tattarowa komai ya shiga, waɗanda suke bayyanar da gaskiyar imani da kuma matuƙar sakankancewa.
  4. Sindi ya ce: Faɗinsa (Kai ne Rayayye) wato: Kai ne wanda ya kamata a nemi tsari da Shi ba waninKa ba.

Manufofin Fassarorin

43 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية