1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan

عَنْ زَيْنَبَ بِنْتِ جَحْشٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْها أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَخَلَ عَلَيْهَا فَزِعًا يَقُولُ:
«لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَيْلٌ لِلْعَرَبِ مِنْ شَرٍّ قَدِ اقْتَرَبَ، فُتِحَ اليَوْمَ مِنْ رَدْمِ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مِثْلُ هَذِهِ» وَحَلَّقَ بِإِصْبَعِهِ الإِبْهَامِ وَالَّتِي تَلِيهَا، قَالَتْ زَيْنَبُ بِنْتُ جَحْشٍ فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ: أَنَهْلِكُ وَفِينَا الصَّالِحُونَ؟ قَالَ: «نَعَمْ إِذَا كَثُرَ الخَبَثُ».

Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa;
"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 3346

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurin Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - a firgice a tsorace, alhali shi yana cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan sanarwa da tinanin afkuwar wani al'amari abin ki da zai faru, kuma babu tsira daga gare shi sai fakewa ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da afkuwarsa ya kusanto, yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju, shi ne katangar da Zulkarnaini ya ginata, misalin wannan; sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda ke biye da shi. Sai Zainab - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Yaya Allah Zai halakar da mu alhali a cikinmu akwai muminai na gari? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Idan barna ta yi yawa da fasikanci da fajirci da sabo, da zina, da giya, da wasunsu, to halaka zata game kowa da kowa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Firgici ba ya shagaltar da mumini daga ambatan Allah a lokacin tsoro; domin da ambatan Allah ne zukata suke nutsuwa.
  2. Kwaɗaitarwa akan hana sabo da hana afkuwarsa.
  3. Halaka mai gamewa tana faruwa saboda sababin yawan sabo da yaɗuwarsa da rashin hanawa koda mutanen kirki sun yawaita.
  4. Masifu suna game mutane baki ɗaya salihai da batattu, saidai za’a tashe su ne akan niyyoyinsu.
  5. Ya kebanci Larabawa a cikin faɗinsa: "Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da ya kusanto"; domin su ne mafi yawan waɗanada suka musulunta lokacin da ya faɗi hakan.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية