1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ:
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ غَدَاةَ الْعَقَبَةِ وَهُوَ عَلَى نَاقَتِهِ: «الْقُطْ لِي حَصًى» فَلَقَطْتُ لَهُ سَبْعَ حَصَيَاتٍ، هُنَّ حَصَى الْخَذْفِ، فَجَعَلَ يَنْفُضُهُنَّ فِي كَفِّهِ وَيَقُولُ: «أَمْثَالَ هَؤُلَاءِ فَارْمُوا» ثُمَّ قَالَ: «أَيُّهَا النَّاسُ، إِيَّاكُمْ وَالْغُلُوَّ فِي الدِّينِ، فَإِنَّما أَهْلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ الْغُلُوُّ فِي الدِّينِ».

Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a washegarin jifan babban shaidan alhali shi yana kan taguwarsa: "Ka tsintomin tsakwankwani". sai na tsinto masa tsakwankwani bakwai, su tsakwankwani ne na harbi, sai ya fara yana motsasu a tafinsa yana cewa: "Misalan wadananan sai ku yi jifa (da su)”. sannan ya ce: "Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku".

Ingantacce ne Ibnu Majah da Nasa'i da Ahmad ne suka ruwaito shi Sunanu Ibn Majah - 3029

Bayani

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - a ranar babbar sallah wayewar garin jifan babban Shaidan a hajjin bankwana, sai ya umarce shi ya tsinto masa tsakwankwanin jifa, sai ya tsinto masa tsakwankwani bakwai, kowacce daya daga cikinsu ta kai girman wake ko bunduq, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya sanya su a hannu sa, sannan ya motsa su, ya ce: Ku yi jifa da kwatankwacin wannan a girma, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar daga wuce gona da iri da tsanantawa da ketare iyaka a al'amuran addini, kadai ketare iyaka da wuce gona da iri da tsanantawa a addini shi ya halaka al'ammomin da suka gabata.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga wuce gona da iri a addini, da bayanin mummunan karshensa, kuma shi ne sababi na halaka.
  2. Izina da wadanda suka rigayemu daga al'ummu dan nisantar abinda suka afka cikinsa na kuskure.
  3. Kwadaitarwa akan koyi da sunna.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
IT Italiano Italiyanci
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية