1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa ‌Ya ke Aisha lallai Allah Mai tausasawa ne kuma Yana son tausasawa, Yana bayarwa akan tausasawa abinda ba Ya bayarwa akan tsanantawa, da kuma abinda ba Ya bayarwa ga waninsa

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رضي الله عنها زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«يَا عَائِشَةُ إِنَّ اللهَ رَفِيقٌ يُحِبُّ الرِّفْقَ، وَيُعْطِي عَلَى الرِّفْقِ مَا لَا يُعْطِي عَلَى الْعُنْفِ، وَمَا لَا يُعْطِي عَلَى مَا سِوَاهُ».

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«‌Ya ke Aisha lallai Allah Mai tausasawa ne kuma Yana son tausasawa, Yana bayarwa akan tausasawa abinda ba Ya bayarwa akan tsanantawa, da kuma abinda ba Ya bayarwa ga waninsa».

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2593

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitawa uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - sauƙi, kuma Allah Mai sauƙi ne Mai sauƙaƙawa bayinSa ne, yana son sauƙi garesu ba Ya so musu tsanani, dan haka ba Ya ɗora musu abinda yafi ƙarfinsu, kuma Yana son bawanSa ya siffantu da tausayi a lamura da kuma riƙo da sauƙi; kada ya zama mai kaushin zuciya mai tsanantawa, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - a duniya Yana bada kyakkyawan yabo da samun abin nema da sauƙaƙa abin nufi saboda sauƙi da tausasawa, a lahira kuma Yana bada gwaggwaɓan lada, sama da yadda Yake bayarwa akan tsanani da kausasawa, sauƙi yana zuwa tare da abinda waninsa ba ya zuwa tare da shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan sauƙaƙawa da kuma hani akan tsanani.
  2. Ɗaukakar matsayin sauƙi tsakanin kyawawan ɗabi'u.
  3. Mai sauƙaƙawa yana cancantar kyakkyawan yabo da kuma gwaggwaɓan lada daga Allah - Maɗaukakin sarki -.
  4. Sindi ya ce: Tsanani kishiyar sauƙi ne, wato wanda yake kiran mutane zuwa ga shiriya da sauƙi da kuma tausasawa ya fi alheri daga wanda yake kiran mutane da tsanani idan bigiren ya kasance yana iya karɓar al'amura biyun, inba haka ba to abinda bigiren yake iya karɓarsa shi ne zai ayyana, Allah ne Mafi sani da haƙiƙanin hali.

Manufofin Fassarorin

37 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية