1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lallai wanda ya fiku soyuwa a gare ni kuma mafi kusancinku mazauni a ranar AlKiyama (su ne) mafi kyawunku halayya

عَنْ جَابِرٍ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ مِنْ أَحَبِّكُمْ إِلَيَّ وَأَقْرَبِكُمْ مِنِّي مَجْلِسًا يَوْمَ القِيَامَةِ أَحَاسِنَكُمْ أَخْلاَقًا، وَإِنَّ أَبْغَضَكُمْ إِلَيَّ وَأَبْعَدَكُمْ مِنِّي مَجْلِسًا يَوْمَ القِيَامَةِ الثَّرْثَارُونَ وَالمُتَشَدِّقُونَ وَالمُتَفَيْهِقُونَ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، قَدْ عَلِمْنَا الثَّرْثَارُونَ وَالمُتَشَدِّقُونَ فَمَا الْمُتَفَيْهِقُونَ؟ قَالَ: «الْمُتَكَبِّرُونَ».

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Lallai wanda ya fiku soyuwa a gare ni kuma mafi kusancinku mazauni a ranar AlKiyama (su ne) mafi kyawunku halayya, kuma mafi ƙinku a gare ni, kuma mafi nisantarku dani a mazauni a ranar AlKiyama masu yawan surutu da masu tsanantawa, da masu jiji da kai», suka ce ya Manzon Allah, haƙiƙa mun san masu yawan surutu da masu tsanantawa to su waye masu jiji da kai ya ce: «Masu girman kai».

Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi Sunan Tirmizi - 2018

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya bayyana cewa yana daga mafi soyuwarku gare shi a duniya, kuma mafi kusancinku mazauni da shi a ranar Alkiyama (su ne) mafi kyawunku a ɗabi'u, kuma cikin mafi ƙiyayyarku gare shi a duniya, kuma mafi nisantarku mazauni daga gare shi a ranar Alkiyama masu munanan ɗabi'u a cikinku; (masu yawan surutu) sune masu yawaita magana dan ɗorawa kai da kuma fita daga gaskiya, (masu tsanantawa kuwa) sune masu yalwatawa a cikin zance dan ɗorawa kai fasaha da girmama maganarsu ba tare da kiyayewa ba, (da masu girman kai). suka ce: Ya Manzon Allah, haƙiƙa mun san masu yawan surutu da masu tsanatwa, to su waye masu jiji da kai? Ya ce: masu girman kai masu yi wa mutane izgili wadanda suke yawaita magana kuma suke bude bakunansu da shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kyawawan ɗabi'u suna daga sabubban soyayyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kusanci da shi ranar Alkiyama, munanan ɗabi'u kuwa akasin haka ne.
  2. Kyawawan ɗabi'u suna daga sabubban soyayyar mutane sashinsu ga sashi, munanan ɗabi'u kuwa akasin haka ne.
  3. Kwaɗaitarwa akan kyutata ɗabi'u da ƙanƙar da kai da rashin kausawa da ɗorawa kai (abinda ya fi ƙarfinta).
  4. Gargaɗarwa daga zance ta ɓangaren yawaitawa da girmamawa da kuma ɗorawa kai (abinda ya fi ƙarfinta).

Manufofin Fassarorin

44 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية