1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce

عَن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«الْحَلِفُ مَنْفَقَةٌ لِلسِّلْعَةِ، مَمْحَقَةٌ لِلرِّبْحِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Muslim - 1606

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi akan rantsuwa da kuma yawaita ta koda ta kasance akan gaskiya ne a siye da siyarwarsa, kuma ya bada labarin cewa ita sababi ce ta yawaitar haja da kaya da kuma samun ribarsu, sai dai hakan tawaya ce kuma ɓata albarkar riba ce da kuma kasuwanci, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai iya dora wasu abubuwa da zasu ɓata su kodai ta hanyar sata ko gobara ko dilmiya a ruwa ko ƙwace ko fizge ko wasu abubuwa masu bijirowa daban waɗanda dukiyarsa zata lalace saboda su.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girmama al'amarin rantsuwa da Allah, kuma cewa ita ba ta kasancewa sai dan wata buƙata.
  2. Kasuwanci na haram koda girmansa ya yawaita; to shi abin cirewa albarka ne babu alheri a cikinsa.
  3. AlƘari ya ce: Tafiyar albarkar abin kasuwanci; kodai dan lalacewa ne wanda zai riske shi a cikin dukiyarsa, ko dan ciyar da shi a abinda anfaninsa ba zai koma zuwa gare shi ba a nan duniya ko ladansa a nan gaba (lahira), ko ya wanzu a wurinsa kuma a haramta masa anfaninsa, ko wanda ba zai gode masa ba ya gaje Shi.
  4. Annawawi ya ce: A cikinsa akwai hani akan yawan rantsuwa a cikin ciniki, domin rantsuwa ba tare da wata buƙata ba abin ƙi ce, kuma zai haɗa da yawaitar haja gare shi, wataƙila mai siye ya ruɗu da rantsuwar.
  5. Yawan rantsuwa tawaya ne a imani, kuma tawaya ne a cikin Tauhidi; domin cewa yawan rantsuwa yana kaiwa zuwa abubuwa biyu: Na farkonsu: Sakaci a cikin hakan da rashin kulawa, al'amari na biyu: Ƙarya, domin cewa duk wanda rantsuwarsa ta yawaita zai afka cikin ƙarya, to ƙaranta hakan yana kamata da kuma rashin yawaita rantsuwa, saboda haka ne tsarki ya tabbatar maSa Ya ce: {Ku kiyaye rantse-rantsenku} [al-Ma'idah: 89].

Manufofin Fassarorin

45 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية