1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta

عَن أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ يُشِيرُ أَحَدُكُمْ عَلَى أَخِيهِ بِالسِّلاَحِ، فَإِنَّهُ لاَ يَدْرِي، لَعَلَّ الشَّيْطَانَ يَنْزِعُ فِي يَدِهِ، فَيَقَعُ فِي حُفْرَةٍ مِنَ النَّارِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta».

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 7072

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi ga musulmi ya nuna ɗan uwansa musulmi da kowane irin makami, domin cewa shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya ɗauke shi akan motsa makamin a hannunsa, sai ya kashe ɗan uwansa ko ya cutar da shi, sai ya faɗa cikin saɓon da zai kai shi ya faɗa cikin ramin wuta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin haramcin jinin musulmi.
  2. Wajabcin girmama musulmi da kiyayewa daga sadar da sharri gare shi ta hanyar aiki ne ko magana, daga hakan akwai nuni da ƙarfe ko da da wasa ne; domin cewa Shaiɗan zai iya zaburar da hannunsa sai ya ƙawata masa dukan ɗan uwansa, ko ya fizge makamin daga hannunsa sai ya faɗa ba tare da zaɓinsa ba sai ya cutar da ɗan uwansa.
  3. Toshe kafa da yin hani daga abinda zai kai zuwa abinda aka haramta.
  4. Kwaɗayi akan zaman lafiyar zamantakewar jama'a da kiyaye alaƙoƙi tsakanin mutane, da rashin tsoratasu koda da nuni ne da kuma yi musu tsawa.

Manufofin Fassarorin

41 Yare
EN English Turanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية