1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FIƘHU DA USULU

Sabuntawa Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri)

عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
مِنَ السُّنَّةِ إِذَا قَالَ الْمُؤَذِّنُ فِي أَذَانِ الْفَجْرِ حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ، قَالَ: الصَّلَاةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ.

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce:
Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri).

Ingantacce ne Ibnu Khuzaimah da Dar Al-Kutni da Baihaki ne suka rawaito shi Sahih Ibnu khuzaimah - 386

Bayani

Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, cewa daga abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tabbatar da shi a cikin sunnarsa, shi ne mai kiran sallah ya ce a cikin kiran sallar Asuba kadai, bayan faɗinsa: (Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira)), ya ce: (Assalatu khairun minan naum (sallah tafi bacci alheri)).

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Faɗinsa: (Yana daga sunnah): Yana nufin sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, to shi yana da hukuncin Raf'u, wato wanda aka danganta shi zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. An so mai kiran sallah a cikin kiran sallar Asuba ya ce bayan ya faɗi: Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira): Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri), sau biyu; domin sallar Asuba a lokacin da mutane suke bacci ne a cikinsa, zasu tashi daga bacci zuwa sallah, sai aka keɓanci sallar Asuba da hakan banda sauran sallolin.

Manufofin Fassarorin

36 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية