1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lallai ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan Lahira, idan mutum ya tsira a cikinsa to abinda ke bayansa ya fishi sauƙi, idan kuma bai tsira a cikinsa ba to abinda ke bayansa ya fi shi tsanani

عَن هَانِئ مَوْلَى عُثْمَانَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: كَانَ عُثْمَانُ إِذَا وَقَفَ عَلَى قَبْرٍ بَكَى حَتَّى يَبُلَّ لِحْيَتَهُ، فَقِيلَ لَهُ: تُذْكَرُ الْجَنَّةُ وَالنَّارُ فَلَا تَبْكِي، وَتَبْكِي مِنْ هَذَا؟ فَقَالَ: إِنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«إِنَّ الْقَبْرَ أَوَّلُ مَنْزِلٍ مِنْ مَنَازِلِ الْآخِرَةِ، فَإِنْ نَجَا مِنْهُ فَمَا بَعْدَهُ أَيْسَرُ مِنْهُ، وَإِنْ لَمْ يَنْجُ مِنْهُ فَمَا بَعْدَهُ أَشَدُّ مِنْهُ».

Daga Hani baran Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Usman ya kasance idan ya tsaya akan ƙabari sai ya yi kuka har sai gemunsa ya yi dan shi, sai aka ce masa: Ana ambatan aljanna da wuta amma baka kuka, kuma kana yin kuka saboda wannan? sai ya ce: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Lallai ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan Lahira, idan mutum ya tsira a cikinsa to abinda ke bayansa ya fishi sauƙi, idan kuma bai tsira a cikinsa ba to abinda ke bayansa ya fi shi tsanani».

Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi Sunan Tirmizi - 2308

Bayani

Sarkin muminai Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya kasance idan ya tsaya akan wani ƙabari sai ya yi kuka har sai hawaye ya sa gemunsa ya yi dan shi, sai akace masa: Ana ambatan aljanna da wuta amma baka kuka dan shauƙi zuwa aljanna ko tsoron wuta! amma kana kuka saboda ƙabari? Sai ya ce: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan lahira, idan ya tsira ya kuɓuta daga cikinsa to abinda ke bayansa na masaukai su ne mafi sauƙi daga gare shi , idan bai tsira daga azabarsa ba; to abinda ke bayansa na uƙuba ya fi tsanani daga abinda ke cikinsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin abinda Usman - Allah Ya yarda da shi - yake a kansa na tsoron Allah - Maɗaukakin sarki - tare da cewa shi yana daga cikin waɗanda aka yi wa albishir da aljanna.
  2. Halaccin kuka a lokacin tina tshin hankali na ƙabari da kuma alƙiyama.
  3. Tabbatar da ni'imar ƙabari da kuma azabarsa.
  4. Tsoratarwa daga azabar ƙabari.

Manufofin Fassarorin

44 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية