1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka

عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ رضي الله عنه قَالَ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ مَا النَّجَاةُ؟ قَالَ: «امْلِكْ عَلَيْكَ لِسَانَكَ، وَلْيَسَعْكَ بَيْتُكَ، وَابْكِ عَلَى خَطِيئَتِكَ».

Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka".

Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi Sunan Tirmizi - 2406

Bayani

Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sabubban tsirar mumini a duniya da lahira?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Na horeka da al'amura uku:
Na farko: Ka kiyaye harshenka daga abinda babu alheri a cikinsa, daga faɗar kowane sharri, kuma kada ka yi wani furuci sai da alheri.
Na biyu: Ka lazimci gidanka dan ka bautawa Allah a cikin kaɗaitakarka, ka shagalta da biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ka nisanci fitinu a cikin gidanka.
Na uku: Ka yi kuka ka yi nadama ka tuba daga abinda ka aikata na zunubai.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin hanyoyin tsira.
  2. Bayanin sabubban tsira a duniya da lahira.
  3. Kwaɗaitarwa akan shagaltar mutum da kansa idan ya gajiya daga anfanar waninsa, ko ya ji tsoron cutarwa akan Addininsa da kansa idan ya cakuɗa da mutane.
  4. Nuni zuwa himmatuwa da gida musamman ma dai a lokacin fitintinu, shi yana daga hanyoyi dan kiyaye Addini.

Manufofin Fassarorin

51 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية