1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«خَيْرُ يَوْمٍ طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ يَوْمُ الْجُمُعَةِ، فِيهِ خُلِقَ آدَمُ، وَفِيهِ أُدْخِلَ الْجَنَّةَ، وَفِيهِ أُخْرِجَ مِنْهَا، وَلَا تَقُومُ السَّاعَةُ إِلَّا فِي يَوْمِ الْجُمُعَةِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a, a cikinsa ne aka halicci (Annabi) Adam, kuma a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, kuma a cikinsa ne aka fitar da shi daga gareta, kuma AlKiyama ba za ta tsayaba sai a ranar Juma'a".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 854

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafificin yinin da rana ta ɓullo a ciknsa shi ne yinin Juma'a. Daga abinda (ginin Juma’a) ya keɓa ta da shi: Allah Ya halicci (Annabi) Adam - aminci ya tabbata agare shi - a cikinsa, a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, a cikinsa ne aka fitar da shi daga aljannar, kuma aka sakko da shi ƙasa, Alkiyama ba za ta tashiba sai a yinin Juma'a.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar ranar Juma'a akan sauran kwanukan mako.
  2. Kwaɗaitarwa akan yawaita ayyuka na gari a cikin ranar Juma'a, da yin tanadi dan samun rahamar Allah - Maɗaukakin sarki -, da tunkuɗe azabarsa.
  3. Waɗannan keɓantattun abubuwan na ranar Juma'a da aka ambace su a cikin Hadisin, wasu malam sun ce: Su ba dan ambatan falalar ranar Juma'a ba ne; domin fitar da (Annabi) Adam da tashin Alkiyama ba'a ɗaukarsu falala. Wasu malaman su ka ce: Kai dukkaninsu falala ce, kuma fitar (Annabi) Adam sababin samun zuriya ne kamar manzanni da annabawa da salihai, tsayuwar Alkiyama kuwa sababin gaggauto da sakamakon salihai ne da samun su ga abinda Allah Ya tanadar musu na karamomi.
  4. An ambaci wasu keɓantattun abubuwa daban ga ranar Juma'a, banda abinda aka ambata a cikin wannan riwayar, daga cikinsu: A cikinta ne aka karɓi tuban (Annabi) Adam, kuma acikinta ne aka ɗauki ransa, kuma aciknta akwai wani (Takaitaccen) lokaci bawa mumini ba zai dace da shi ba yana sallah (Addu’a) yana roƙon Allah wani abu ba sai Ya amsa masa.
  5. Mafificin yini a shekara ranar Arfa, (wasu malaman) suka ce: Ranar babbar sallah, kuma mafificin kwanukan mako ranar Juma'a, mafificin darare kuma daren Lailatul Kadr.

Manufofin Fassarorin

56 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية