1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Ka guji duniya sai Allah Ya so ka, ka guji abin da ke hannun mutane sai mutane su so ka

عَنْ أَبِي العَبَّاسِ سَهْلِ بْنِ سَعِدٍ السَّاعِدِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، دُلَّنِي عَلَى عَمَلٍ إِذَا عَمِلْتُهُ أَحَبَّنِي اللَّهُ وَأَحَبَّنِي النَّاسُ، فَقَالَ:
«ازْهَدْ فِي الدُّنْيَا يُحِبُّكَ اللَّهُ، وَازْهَدْ فِيمَا عِنْدَ النَّاسِ يُحِبُّكَ النَّاسُ».

Daga Abul Abbas Sahlu ibnu Sa'ad al-Sa'idi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, ka shiryar da ni akan aikin da idan na aikata shi Allah zai soni mutane ma za su so ni, sai ya ce:
«Ka guji duniya sai Allah Ya so ka, ka guji abin da ke hannun mutane sai mutane su so ka».

Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah da waninsa ne suka ruwaito shi da isnadai kyakkyawa Arba’una Annawawi - 31

Bayani

Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi zuwa aikin da idan ya aikata shi Allah zai so shi kuma mutane ma zasu so shi, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Allah zai so ka idan ka bar mafifici a duniya, da abin da ba zai amfaneka a lahira ba, kuma ka bar abin da zai iya yi wuwa a cikinsa akwai cutarwa a Addinika, kuma mutane zasu so ka idan ka guji abinda ke hannunsu na duniya; domin su a ɗabi'arsu suna sonta, wanda kuwa ya yi gogayya da su a kanta zasuƙi shi, wanda ya bar musu ita zasu so shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar gujewa duniya, shi ne: Yabar abin da ba zai amfanar a lahira ba.
  2. Gudun duniya darajarsa ta fi tsantseni; domin cewa tsantseni shi ne barin abin da zai iya cutarwa, gudun duniya kuwa shi ne barin abin da ba zai amfanar a lahira ba.
  3. Sindi ya ce: Lallai cewa duniya abar so ce a wurin mutane, duk wanda ya yi gogayya da su a cikinta zai zama abin ƙi a wurinsu gwargwadan haka, wanda kuma ya barsu da abar sonsu zai zama abin so a cikin zukatansu gwargwadan hakan.

Manufofin Fassarorin

58 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
FR Français Fassara Yaren Faransanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
DA Dansk الدنماركية
RN Kirundi الكيروندي
KMR Kurmancî الكرمنجية
MS Bahasa Melayu الملايو