عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِيَّاكُمْ وَمُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ، فَإِنَّمَا مَثَلُ مُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ كَقَوْمٍ نَزَلُوا فِي بَطْنِ وَادٍ، فَجَاءَ ذَا بِعُودٍ، وَجَاءَ ذَا بِعُودٍ، حَتَّى أَنْضَجُوا خُبْزَتَهُمْ، وَإِنَّ مُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ مَتَى يُؤْخَذْ بِهَا صَاحِبُهَا تُهْلِكْهُ».

Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Na haneku da ƙananan zunibai, kaɗai misalin ƙananan zunubai kamar mutane ne da suka sauka a cikin wani kwari, sai wannan ya zo da ice, wannan ma ya zo da ice, har suka sa gurasarsu ta nuna, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu saboda su zasu halaka shi».

Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi Musnad Ahmad - 22808

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga sakaci a aikata ƙananan zunubai, da kuma yawaitasu domin cewa su idan sun taru zasu halakar, kuma ya buga misali akan hakan da wasu mutanen da suka sauka a cikin wani kwari, sai kowanne daga cikinsu ya zo da ita ce ƙarami, har sai da suka sa gurasarsu ta nuna saboda taruwar abinda suka tara na itatuwan, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu da su bai tuba daga garesu ba ko kuma Allah bai yi masa afuwa ba to zasu halaka shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a buga misalai dan kusanto da fahimta da kuma ƙara bayani.
  2. Gargaɗarwa daga ƙananan zunubai waɗanda ake wulaƙantar da su, da kuma kwaɗaitarwa akan gaggawar kankare su.
  3. Ƙanana zunubai suna ɗaukar ma'anoni: Na farko: Abinda bawa yake aikata shi cikin zunubai, yana mai ɗimuwar cewa shi ƙarami ne, alhali shi yana cikin manyan zunubai a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -. Na biyu: Abinda bawa yake aikata shi daga ƙananan zunubai ba tare da kulawa da su ba, sai waɗannan ƙananan zunuban su taru a kansa har sai sun halaka shi. Na uku: Abinda bawa yake aikata shi na ƙananan zunubai, ba ya kulawa da su, sai su zama sababi dan afkawarsa a cikin manyan zunubai masu halakarwa.

Manufofin Fassarorin

41 Yare
EN English Turanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية