1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِذَا رَأَى أَحَدُكُمُ الرُّؤْيَا يُحِبُّهَا فَإِنَّهَا مِنَ اللَّهِ، فَلْيَحْمَدِ اللَّهَ عَلَيْهَا وَلْيُحَدِّثْ بِهَا، وَإِذَا رَأَى غَيْرَ ذَلِكَ مِمَّا يَكْرَهُ، فَإِنَّمَا هِيَ مِنَ الشَّيْطَانِ، فَلْيَسْتَعِذْ مِنْ شَرِّهَا، وَلاَ يَذْكُرْهَا لِأَحَدٍ، فَإِنَّهَا لَنْ تَضُرَّهُ».

Daga Abu Sa'id Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba".

Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 7045

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, kuma ya nunar da cewa ya godewa Allah akansa, ya kuma bada labarinsa, idan kuma ya ga abinda yake ƙinsa yake baƙanta masa rai to shi kawai daga Shaiɗan ne; to ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ya faɗawa kowa; (to mafarkin) ba zai cutar da shi ba , inda Allah Ya sanya abinda aka ambata sababi na kuɓuta daga abinda yake na mugun mafarkin .

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Rabe-raben mafarki: 1- Kyakkyawan mafarki, shi ne mafarki na gaskiya kuma bushara daga Allah da (mutum) yake ganinsa ko agane masa, 2- Zancen zuci shi ne abinda mutum yake zantar da kansa a farke, 3- Baƙantawa da tsoratarwar Shaiɗan da razanarwa daga gare shi dan ya baƙanta ran ɗan Adam ne.
  2. Abinda aka ambata a taƙaice a Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku: Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
  3. Abinda aka ambata a taƙaice daga ladabin mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar: Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa mafarkin, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba.
  4. Ibnu Hajar ya ce: Hikima a cikinsa cewa shi idan ya fadawa wanda ba ya ƙauna kyakkyawan mafarki zai iya fassara masa da abinda ba ya so kodai dan ƙiyayya ko dan hassada, kuma zai iya faruwa akan waccan siffar ko ya gaggautowa kansa baƙin ciki da takaici daga hakan, to sai aka umarce shi da barin fadawa wanda ba ya so saboda hakan.
  5. Godiya a yayin faruwar ni'imomi, da sabuntuwar abubuwan buri, to hakan sababi ne na dawwamar su.

Manufofin Fassarorin

51 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية