1. Gida
  2. kashe kashe
  3. FALALOLI DA LADUBBA

Sabuntawa Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta

عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يَبْسُطُ يَدَهُ بِاللَّيْلِ لِيَتُوبَ مُسِيءُ النَّهَارِ، وَيَبْسُطُ يَدَهُ بِالنَّهَارِ لِيَتُوبَ مُسِيءُ اللَّيْلِ، حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا».

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2759

Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuba daga bayinSa. Idan bawa ya yi laifi da rana kuma ya tuba da daddare Allah Zai karbi tubansa, idan ya yi laifi da daddare ya kuma tuba da rana Allah Zai karɓi tubansa. Kuma tsarki ya tabbatar maSa Yana shinfiɗa hannunSa dan tuba dan farin ciki da tuban, da kuma karɓar tuban, ƙofar tuba tana nan a bude har sai rana ta ɓullo daga yammacinta dan alamtar wa da ƙarewar duniya, idan ta ɓullo to za'a kulle ƙofar tuba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Karɓar tuba yana nan muddin ƙofar na nan a buɗe, kuma ana kulle ƙofarta ne da ɓullowar rana daga mafaɗarta. Kuma idan mutum ya tuba kafin gargarar mutuwa, shi ne rai ya kai maƙogwaro.
  2. Rashin yanke ƙauna saboda zunubi, domin cewa afuwar Allah - tsarki ya tabbatar maSa - da rahamarSa masu yalwa ne, kuma ƙofar tuba abuɗe take.
  3. Sharuɗɗan tuba: Na ɗaya: Barin aikata laifin. Na biyu: Nadama akan aikata shi. Na uku: Kudirce niyya akan ba zai koma zuwa gare shi ba har abada. Wannan idan ya kasance a cikin haƙƙoƙin Allah - Maɗaukakin sarki - ne, idan ya kasance ya rataya da haƙƙin wani daga haƙƙoƙin bayi, to an sharɗanta ga ingancin tuban ya mayar da wannan haƙƙin ga mai shi, ko mai haƙƙin ya yi masa afuwa.

Manufofin Fassarorin

56 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá Yoruba
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية