1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa

عَنْ أَبِي طَلْحَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ تَدْخُلُ المَلاَئِكَةُ بَيْتًا فِيهِ كَلْبٌ وَلاَ صُورَةٌ».

Daga Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 3322

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'ikun rahama ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoton masu rayuka; Hakan cewa hoton abinda yake da rai: Saɓo ne mai muni, kuma a cikinsa akwai kamanceceniya da halittar Allah, kuma hanya ce daga hanyoyin shirka, wasu daga cikinsu hoton abinda ake bautawa ne koma bayan Allah. Amma sababin hanuwarsu daga (shiga) gidan da a cikinsa akwai kare: Saboda yadda yake yawan cin najasa, kuma sashinsu an ambace shi Shaiɗan; mala'iku kishiyotin shaiɗanu ne, saboda munin warin kare; mala'iku suna ƙin mummunan wari, kuma su (karnuka) an yi hani daga kiwonsu; sai aka yi wa mai riƙonsu ukuba da haramcin shigar mala'ikun rahama gidansa, da sallarsu a cikinsa, da nema masa gafara, da sa albarkarsu gare shi da kuma cikin gidansa, da tunkuɗewarsu cutar Shaiɗan daga gare shi .

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin riƙon kare sai dai karen farauta ko gadin dabbobi ko gona.
  2. Riƙon hotuna suna daga al'amura munana waɗanda mala'iku suna guduwa daga garesu, kuma samunsu a guri sababi ne na haramcin rahama, kwatankwacin haka a kare.
  3. Mala'ikun da ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoto sune mala'ikun rahama, amma masu gadin (mutane) da wasunsu daga waɗanda suke da wani aiki kamar mala'ikan mutuwa to su suna shiga kowane gida.
  4. Haramcin rataya hotonan masu rayuka a bangwaye da wasunsu.
  5. AlKhaɗɗabi ya ce: Kaɗai mala'iku basa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoto daga abinda riƙonsa yana haramta na karnuka da hotuna, amma abinda ba haramun bane na karen farauta da gona da kiwo, da hoton da ake wulaƙantasu a shinfiɗu da matasai da wasunsu to shigar mala'iku ba ya haramtuwa saboda shi.

Manufofin Fassarorin

53 Yare
EN English Turanci
UR اردو urdu
ES Español Sifaniyanci
ID Indonesia Indonisiyanci
UG ئۇيغۇرچە Uighur
BN বাংলা Fassarar Bangaliyanci
TR Türkçe Turkiyanci
RU Русский Rashanci
BS Bosanski Bosniyanci
SI සිංහල Sinhalese
HI हिन्दी Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
ZH 中文 Fassara da Yaren Chanise
FA فارسی Farisanci
VI Tiếng Việt Vietnam
TL Tagalog Tagalog
KU Kurdî Kurdawa
PT Português Portuguese
ML മലയാളം Malayalam
TE తెలుగు Telgonci
SW Kiswahili Swahili
TA தமிழ் Yaran Tamili
MY မြန်မာ Yaran Barma
TH ไทย Yaran Tailand
DE Deutsch Jamusanci
PS پښتو bushtu
AS অসমীয়া Asami
SQ Shqip Albaniyanci
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча Kirgisisch
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda Kinyarwanda
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy Malagasy
OM Oromoo Oromo
KN ಕನ್ನಡ Kanadische Übersetzung
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan Aserbaidschanisch
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية